– Dan takarar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana cewa ‘yan PDP na nema su kai masa hari a wurin kamfen
– Obaseki yace an kama wasu tsageru da aka dauko haya a mota don su kai masa hari wajen yakin neman zabe a garin Benin, wani babban birnin jihar Edo
– Wani dan asalin jihar Edo yace ba tantama APC ce za ta lashe zaben gwamnan jihar da za ayi a ranar Asabar, 28 ga watan Satumba
Godwin Obaseki, dan takarar gwamnan jihar Edo a karakashin Jam’iyyar APC yace wasu nema su ga bayan sa. Obaseki yace ‘yan PDP ne suke neman su ga karshen rayuwar sa.
A cewar dan takarar gwamnan jihar ta Edo, ‘yan Jami’iyyar PDP din sun shirya kai masa hari a hanya lokacin da yake kokarin yakin neman zaben Jihar. Obaseki yace sai dai Ubangiji ne kawai ya taimake sa, jami’an tsaro sun dauki mataki da wuri.
KU KARANTA: Rikicin Jam’iyyar PDP ya zo karshe
Dan takarar gwamnan jihar Edo na APC, Godwin Obaseki yace Jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga wani hali musamma a bangaren Edo ta tsakiya, don mutane da dama sun tsere sun bar Jam’iyyar. Godwin Obaseki na Jam’iyyar APC yace alkaluma sun nuna APC za ta ci zaben na Gwamnan Jihar Edo da kusan kashi 75%. The Nations ta rahoto dan takarar Gwamnan yana cewa za su buge PDP raga-raga a ranar 28 ga watan Satumban nan.
Godwin Obaseki yake cewa har a inda PDP take tunani tana da karfi APC za ta buge Jam’iyyar PDP din, irin su Arewacin jihar.
Obaseki yace a wurare kadan ne kawai Jam’iyyar ta APC ba za ta buge PDP ba. Godwin Obaseki idan har za ayi zabe na gaskiya, ba tare da tashin hankali ba don a ce za a dage zaben, APC za tayi nasara.
The post Dan takarar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki yace ‘yan PDP na nema su kashe shi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cQKKpR
via IFTTT