An kai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kotu

– Wani lauya mai suna Daniel Makolo, ya kai karar Shugaban kasa Muhammadu Buhari kotu saboda rashin wani dan jihar Kogi a majalisar zartarwa ta tarayyar kasar

– Lauyan yana kara cewa rashin dan jihar Kogi a majalisar zartarwar yunkuri ne tauye masu hakkin su

– Lauya Mokolo yace akwai nauyi a wuyan shugaban kasar na nada minista guda daga kowace jiha cikin jihohin kasar nan

James-Ocholi

 

 

 

 

 

Wani lauya mai suna Daniel Makolo ya shigar da karar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya garzaya ya nada minista daga jihar Kogi.

Lauyan dai ya kai karar Shugaba Buhari ne saboda dalilin rashin wani dan jihar Kogi a cikin majalisar zartarwa ta tarayyar kasar.

Lauya Daniel Makolo ya maka karar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Babban Kotun Tarayya da ke Lokoja, karar mai lamba FHC\L\CS\44\2016 na neman a matsawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da yayi abin da ya dace. Hukumar dillacin labarai na Kasa watau NAN ta rahoto wannan labari.

KU KARANTA: Taron UN: Bambancin fitar Jonathan da Buhari

Tun bayan rasuwar James Ocholi dai har yanzu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai nada wani sabon Minista da zai maye gurbin na sa ba. Marigayi Ocholi ya rika matsayin Karamin Ministan samar da aikin yi kafin rasuwar sa a wani hadarin mota. Hakan ne yasa wannan lauya yake neman Kotu ta sa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wani dan Jihar Kogi a madadin sa.

Lauya Makolo yace kin nada wani sabon Minista dai ya saba dokar Kasa, hakan kuma ba daidai bane, bai dace ba. Makolo yace da haka ana nema a tauye hakkin mutanen Jihar Kogi wajen duk wani taro na Majalisar zartarwa ta Tarayyar Kasar nan. Lauyan na nema a tursasa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada wani sabon Ministan cikin gaggawa, haka kuma a ruguje duk wani mataki da aka dauka lokacin da Jihar Kogi ba ta da wakili. Lauyan kuma yana bukatar an binciki mutuwar James Ocholi.

The post An kai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kotu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cVTA36
via IFTTT


SHARE THIS
Previous Post
Next Post