Ayo Fayose ya kai ziyara Aso Rock

– Gwamna Ayo Fayose ya hallarci taron NEC a fadar shugaban kasa da ke Birnin Tarayya, Abuja

– Halartar wannan taro ta ba jama’a mamaki, domin kuwa gwamnan jihar Ekiti Fayose bai saba zuwa fadar shugaban kasar ba

– Taron dai ya shafi zartarwa game da harkar tattalin arzikin kasa

Fayose Ayo

 

 

 

 

 

 

Gwamna Ayo Fayose ya hallarci fadar shugaban kasa wato Aso Villa domin wani taro na harkar tattalin arzikin kasa, yayin da dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana can kasar Amurka wajen taron majalisar dinkin duniya da ake yi.

Gwamna Fayose na jihar Ekiti tare da sauran gwamnonin kasar nan sun hallarci taron na NEC da aka yi jiya, Alhamis, 22 ga watan Satumba a birnin Abuja.

KU KARANTA: Buhari ne babbar matsalar Najeriya, Inji Fayose

Abin ya ba jama’a mamaki domin kuwa gwamnan bai cika zuwa wannan taron da aka saba yi ba a fadar Villa ta shugaban kasa. Sai dai ko yanzu din gwamnan ya je ne yayin da Shugaba Buhari yana Amurka wajen taron majalisar dinkin duniya watau UN.

A cikin watan Maris na wannan shekarar, Fayose ya hallarci wani taron bita da aka yi a fadar ta Villa, sai dai ana tsakiyar taron gwamnan ya fice abin sa. Gwamna Fayose ya fadawa ‘yan jarida cewa abin duk shirmen banza ne kawai.

A wancan lokaci, Fayose yace anyi asarar kudin jama’a ne kawai har naira miliyan 250 wajen gudanar da abin da ba sa da amfani. Yace dama gwamnati za ta karkatar da irin wannan kudi zuwa ga ‘yan kasuwa masu karamin hannun da bai wuce cinikin N5000 ba.

Gwamnan yace yanzu idan za a raba N10000 har miliyan 250 ga masu cinikin borkono, sai mutane 25,000 sun amfana.

Fayose dai bai ce komai ba ga ziyarar da ya kai fadar Aso Rock din ta shugaban kasa ba.

The post Ayo Fayose ya kai ziyara Aso Rock appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2d99gBS
via IFTTT


SHARE THIS
Previous Post
Next Post