Fadar shugaban kasa tayi bayani game da tafiyar iyalin Buhari Amurka (HOTUNA)

A ranar Laraba, 21 ga watan Satumba ne mai magana da yawun Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu yayi bayani dangane da tafiyar iyalin Shugaba Buhari zuwa ga kasar Amurka.

Aisha Buhari tare da Halima da Zahra Buhari

Aisha Buhari tare da Halima da Zahra Buhari

An hangi yayan shugaban kasa Zahra da Halima Buhari tare da Uwargidarsa Aisha Buhari a dakin taron majalisar dinkin Duniya, wanda hakan yayi matukar harzuka yan Najeriya.

KU KARANTA: Yusuf da Zahra Buhari sun kammala karatunsu a Birtaniya

Shehu yace gwamnati bata biya ko sisinta ba wajen tafiyan iyalan shugaban kasa Buhari ba, asali ma da kansu suka biya kudaden su, sai dai bai nuna wani shedan haka ba.

Adetutu-Balogun

Hakazalika Shehu yaki bayyana dalilin daya sa suka halarci taron majalisar dinkin duniya. Ba’a taba ganin wani shugaban kasa ya tafi da yayansa taron majalisar dinkin duniya ba.

Duk da an fadi cewa Aisha Buhari ita ta biya ma kanta kudin tafiya, wasu yan Najeriya sun nuna bacin ransu game da tafiyar musamman a wannan lokacin karayar tattalin arziki.

buhari-UN-3-copy

Aisha Buhari tare da yayanta Zahra da Halima sun raka shugaba Buhari taron majalisar dinkin duniya karo na 71 daya gudana a garin New York kasar Amurka, baya ga ganawa da shuwagabannin kasashen Duniya,  Ana sa ran shugaba Buhari zai halarci wasu tarurruka na daban wadanda suka shafi bukatun Najeriya.

The post Fadar shugaban kasa tayi bayani game da tafiyar iyalin Buhari Amurka (HOTUNA) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2d77Wzi
via IFTTT


SHARE THIS
Previous Post
Next Post