– IPOB,MASSOB sun juya bayansu ga shirin zanga-zangar da Rediyo Biafara ke shirin yi
– Kungiyoyin sunce shirme ne tunda sun zauna a kasan waje ,sun bar Igbo na mutuwa a gida
– Sunyi kira da yan kabilan igbo su cigaba da ayyukan yau da kullun
?????????????
Gamayyar kungiyan Indigenous People of Biafra (IPOB) and the Movement for the Actualisation of Sovereign State of Biafra (MASSOB) sunyi kaca-kaca da masu da’awar a zauna a gida ranan juma’a ,23 ga watan Stumba.
Wata shirin da aka gabatar a gidan Rediyon Biafra tayi kira yan kabilan igbo da ke zaune a yankin kudu maso gabas da su zauna domin zanga-zanga akan cigaba da tsare Nnamdi Kanu, diraktan Rediyo Biafra kuma Shugaban IPOB.
NAN ta bada rahoton cewa a wata jawabin da shugaba da sakataren gamayyar suka sanya hannu , Messrs Okanu Muoneme da Basil Okwu, sun ce duk da cewa sakin Nnamdi Kanu ne manufar su, ba zasu yarda da mutuwar mutanensu bah aka kawai.
Wata zanga-zangar yakin neman Biyafara ya zama rigima ne tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a ranan litinin ,30 ga watan Mayu.
Kana gamayyar tayi kira ga gwamnatin tarayya akan kawo cigaba yankin kudu maso kud da kudu maso gabas.
KU KARANTA: An tsinci gawar dan Najeriya a lungun tayar jirgin Saudi
“Mu IPOB da MASSOB, munyi murabus da maganganu rediyon biyafara cewa mutanen mu su zauna a gida a ranan 23 ga watan satumba domin zanga-zangar sakin Nnamdi Kanu.
“Muna mika kokon baran mu ga shugaba Buhari da ya saki Nnamdi Kanu ba tare da wasu sharruda ba kuma abi umurnin kotu bada dadewa ba. Muna kira ga mutane su cigaba sa ran Biafra a zuciya kuma su fita kasuwancin su.
“Abun kunya ne cewa da yawa daga cikin mambobinmu sun mutu kuma saura na cikin kurkuku yayinda kalilan mutane ke aikin rediyo Biafra. Ba zamu yarda mu zamar da kamnu aladu ba.”
Zanga-zangar neman yancin biyara a kwanakin baya na barkewa zuwa hayaniya inda ake rasa rayukan jama’a. a wata zanga-zanga da aka yi a Onitsha an rasa rayuka 30,an kuma jefa yan sanda 2 rafin Neja. Sanadiyar haka, kasuwanci ta tsaya, motoci suka daina motsi sanadiyar kona tayoyi da aka yi.
The post IPOB, MASSOB sunyi kaca-kaca da Rediyo biyarafa akan zanga-zanga appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2coXZaO
via IFTTT