– Wata Makarantar fina-finai ta Afrika ta fitar da kasida game da harkar wasan kwaikwayo a Kasar
– Kasidar na kunshe da gabatarwa daga bakin Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari
– A mukkadimar ta sai ya kira Kungiyar ta Nollywood ta cigaba da bada hadin kai ga Gwamnati
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
‘African Film Academy’ ta fitar da wata kasida game da Harkar fina-finai a Kasar Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bada gabatarwa a wannan takardar. Shugaba Buhari yace Nollywood ta fara ne daga wasu tsirarrun matasa masu basira har ta kai matsayin irin su Bollywood da Nollywood na Kasar Amurka da India.
Shugaba Buhari yace kamar wasa Nollywood yanzu ta rika, ta zama hanyar cin abincin dubban mutane a Kasar, hakan ta sa Nollywood ke kara habaka karfin tattalin arzikin Kasar Najeriya da ake kira GDP. Shugaba Buhari yayi alkawarin cigaba da goyon-bayan Nollywood, ya kuma yi kira ga wadanda ke cikin harkar da su yi kokarin fito da Najeriya, kuma su rika shirye fina-finai masu tasiri wajen fadakar da al’umma, ba kawai wasan kwaiwayo mara amfanin komai ba.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi magana game da sabon bidiyon Boko Haram
Shugaba Buhari yace abin da ya kamata shine, a rika shirya fina-finai da za su nuna inda muka yi fice, Fina-finai da za su rika nuna amfanin ilmi a Kasa, fina-finai masu dauke da sakon cewa bai dace a ci zarafin ‘ya ‘ya mata ba dai da sauran su. Buhari yace ba ya shakka ko kadan cewa nan gaba ma sai Nollyeood ta zarce haka.
Shugaba Buhari yace dai bai kamata kuma Nollywood su rika kaucewa tsarin al’ummar mu, da kuma addinin mu ba. Don haka dole a guji abubuwan da za su shafi tsaraici da makamantan su. Dole kuma a guji kawo kabilanci ko nuna wani bambanci a cikin wasa.
The post Kar ku gurbata mana tarbiyya-Shugaba Buhari ya kira Nollywood appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cSw2wv
via IFTTT