Real Madrid da Villareal sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a gasar La Liga mako na biyar da suka kara a ranar Laraba.
Madrid ce ta fara cin kwallo ta hannun Sergio Ramos, yayin da Villareal ta farke ta hannun Bruno Soriano a bugun fenariti.
Da wannan sakamakon Villareal ta taka wa Madrid yawan lashe wasannin La Liga da ta yi 16 a jere.
Madrid din ta kafa tarihin lashe wasannin La Liga 16 a jere a ranar Lahadi, bayan da ta ci Espanyol 2-0, kuma ta yi kan-kan-kan da Barcelona wadda ta fara kafa tarihin a 2010/11.
Mai karatu zai iya tunawa dai cewa a jiya ne Villareal za ta ziyarci Real Madrid a gasar La Liga wasan mako na biyar da za su kara a ranar Laraba.
Madrid tana mataki na daya a kan teburin gasar da makin 12, yayin da Villareal ke matsayi na shida da maki takwas.
A ranar Lahadi Real Madrid ta yi kan-kan-kan da Barcelona a yawan lashe wasannin La Liga 16 a jere, bayan da ta ci Espanyol 2-0.
Sauran wasannin mako na biyar a gasar ta La Liga da za a yi a ranar Laraba, Barcelona za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a Camp Nou.
Barcelona tana mataki na biyu da maki tara, ita kuwa Atletico maki takwas ne da ita tana matsayi na hudu a kan teburin La Liga.
The post Real Madrid ta samu babban cikas (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cFPYzm
via IFTTT