Okorocha yayi ma yan wasan nakasassu kyautan mota da N1m

An yaba ma gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha sakamakon halin arziki daya nuna ma yan wasan ‘Paralympic’ wato olimfik din nakasassu da suka fito daga jihar Imo su uku.

Rochas yayin da yake nuna zinaren da yan wasan suka ciyo

Rochas yayin da yake nuna zinaren da yan wasan suka ciyo

Yan wasan da suka lashe zinaren

Yan wasan da suka lashe zinaren

Jaridar National Helm ta ruwaito gwamnan ya baiwa kowane dan wasan daya lashe Zinariya a cikinsu kyautan naira miliyan 1 da mota, yan wasan kuwa sune Roland Ezurike, Nwosu Ndidi da Orji Josephine Precious. sa’annan gwamnan yayi ma masu horar da yan wasan ma kyauta.

Su ko yan wasan, rera ma gwamnan wakar suka yi sakamakon a ranar yake bikin cika shekaru 54, inda suka yi alkawarin kara zage damtse a kan harkar wasanni.

vllkyt514t54hs8br.783bf0b0

Yayin da Okorocha ke jawabi yace “duk wani kyakkyawan abu da zai faru a Najeriya daga Imo yake zuwa, kuma jihar Imo na alfahari daku.” NAIJ.com ta ruwaito Roland Ezuruike ta kafa tarihi har guda uku inda ya lashe zinari a wasan daga karfe mai nauyin kilo 54, inda Ndidi Nwosu ta lashe kyautan zinari a wasan daga karfe mai nauyin kilo 140, Josephine Orji ta lashe kyautan zinari a wasan daga karfe mai nauyin kilo 86.

KU KARANTA: Nakasashen Dan Najeriya Ezuruike ya ci zinariya a Rio

Da fari su ma yan majalisar wakilan kasar nan sunyi alkawarin baiwa yan wasan ‘Paralympic’ kyautan naira miliyan 18, ma’ana dukkanin yan majalisa su 360 zasu bayar da naira dubu hamsin 50,000 kenan ga yan wasan sakamakon nasarar da suka samu a gasar.

vllkyt9li702jj088.fe86aa68vllkyt7qeplbs77tu.fe56a279

Najeriya ta zamo kasa ta 17 a jerin kasashen da suka lashe kyatuka daban daban, inda ta lashe kyautan zinari guda takwas, azurfa 2, da tagulla 2, hakan ke nuna wannan shi ne mafi nasarar da kasar ta taba samu tun bayan fara gasar a 1992 a birnin Barcelona.

The post Okorocha yayi ma yan wasan nakasassu kyautan mota da N1m appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cHM4FS
via IFTTT


SHARE THIS
Previous Post
Next Post