“Kana da mutunci a idon Duniya”- Ban Ki Moon ga Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wata ganawa da sakataren majalisar dinkin Duniya Ban Ki-Moon a yayin babban taron majalisar karo na 71 daya gudana a kasar New York.

vllkyt4r5lbnr9flt.8bdf18c2

Ban Ki-Moon bayyana ma Shugaba Buhari cewa shuwagabannin duniya na ganin shi da mutunci matuka, sa’annan ya kara da yaba ma shugaba Buhari dangane da yaki da cin hanci da rashawa da yake yi, da kuma yakin kungiyar ta’addanci na Boko Haram. Ban Ki Moon ya jaddada ma Buhari cewa shuwagabannin Duniya suna jin mai saboda dawowa ma kasar Najeriya mutuncinta da yayi.

Sakataren yace “kana da mutunci a idon shuwagabannin kasashen duniya, ciki har da ni. Mutuncinka ya daga mutuncin kasarka a idanun Duniya.” A cewar Ban Ki Moon, majalisar dinkin duniya tana sane da nasarorin da Shugaba Buhari ya samu akan kungiyar Boko Haram, inda ya bada shawarar a dinga kula da hakkin bil adama don kauce ma faruwar irin abinda ke faruwa a kasar Syria.

Shugaba Buhari, minista Amina da Ban Ki Moon

Shugaba Buhari, minista Amina da Ban Ki Moon

KU KARANTA: Dalilai daya sanya na Kagara Inga Buhari – Ban Ki-Moon

A ranar Lahadi 18 ga watan satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin NewYork domin halartar babban taron majalisar dinkin duniya karo na 71, shugaba Buhari ya gana da takwararsa na kasar Amurka, Barack Obama a ranar talata 20 ga watan satumba inda suka tattauna batun matsalar tsaro dake addabar Najeriya.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaba Buhari ke halartan taron majalisar dinkin Duniya tun bayan kasancewarsa shugaban kasar Najeriya.

The post “Kana da mutunci a idon Duniya”- Ban Ki Moon ga Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2d4Srqv
via IFTTT


SHARE THIS
Previous Post
Next Post