– Tsagerun ‘Niger Delta Avengers’ (NDA) sun gargadi gwamnatin tarayya da ta fa san da wadanda ta ke yin tattaunawar sulhu
– Kungiyar ta NDA ta gargadi Shugaba Buhari da ya bi a hankali wajen zaman da yake yi da ‘yan yankin na Neja-Delta
– ‘Yan Niger Delta Avengers’ sun kira Shugaba Buhari da ya bi a hankali kar ya shiga hannun mutanen bogi wajen yarjejeniyar sulhun da ake yi tsakanin gwamnati da tsagerun yankin na Neja-Delta
Tsagerun Niger Delta Avengers sun gargadi Shugaba Muhammadu Buhari da ya lura da wadanda yake zaman ganawar sulhu da su, da sunan tsagerun Neja-Delta. Ana dai kokarin samun yarjejeniyar sulhu ne tsakanin tsagerun yankin da suka addabi kasar da kuma gwamnatin tarayya.
KU KARANTA: EFCC na binciken Dame Patience
Tsagerun sun kira Shugaban Kasar da ya guji zama da Sarakunan gargajiya domin wata yarjejeniya.
Tsagerun NDA sun ce lallai idan Gwamnatin Tarayya ba ta bi a hankali ba wajen zaman kawo sulhun da take yi, za ta fada hannun mutanen banza. Kungiyar dai ta sha daukan nauyin duk wasu barna da ake yi a yankin na Neja-Delta mai arzikin mai, tsagerun su kan fasa butatan man kasar da ke yankin.
KU KARANTA: Shin Mulkin Kasar nan gadon Arewa ne?
Sahara Reporters ta rahoto cewa tsagerun NDA din sun yi wani jawabi a jiya ta bakin wani Kanal Rightman Hudson Opukurowari, tana mai cewa lallai gwamnati ta zauna ne da kwamitin su Wole Soyinka da kuma Anthony Ani.
Kanal Opukurowari yace Kungiyar NDA ta bayyana mutanen da ta wakilta da su zauna ayi suyi sulhu da gwamnati a madadin ta. Sai dai kuma duk da haka suna jin wani labari na dabam.
Kungiyar ta gargadi gwamnati karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasa da ta guji wata tattaunawa da duk wasu sarakunan yankin ko dattawan su irin su Cif Edwin K. Clarke, King Alfred Diete Spiff, Tony Uranta Da su Cif Ajumogobia, dsr. Kungiyar tace wadannan ba mutanen ta bane.
The post Tsagerun Niger Delta Avengers sun gargadi gwamnatin tarayya saboda hakan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2dexAhL
via IFTTT