UN: Shugaba Buhari ya sa hannu a wata yarjejeniya

– Mai magana da bakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a wata takardar Paris ta yarjejeniyar sauyin yanayi.

– Adesina yace wannan duk yana daga cikin kokarin Shugaba Buhari na ganin kasar Najeriya ta hada kai da sauran Kasashen duniya wajen magance matsalar da sauyin yanayi yake kawowa.

– Shugaba Buhari yayi wannan jawabi ne yayin da yake magana ga mahalarta taron na Majalisar dinkin (UNEP) duniya a Birnin New York.

PMB UN

 

 

 

 

 

 

Shugaba Buhari na Najeriya ya sa hannu bisa yarjejeniyar rage fitar da bakar iska mai cutarwa, wannan yarjejeniyar za ta sa a rage fitar da iskar da ke cutarwa (ta mota ko sauran abubuwa masu amfani da man fetur dsr) da kashi 20 zuwa 45 cikin 100.

Shugaba Buhari yake cewa wannan gagarumin abu ne bayan ya sa hannun. Buhari ya kuma tabbatar da cewa yana sa rai kasashen za su cin ma wannan buri.

KU KARANTA: Shugaba Buhari wajen taron UN a New York

Shugaban Kasan Najeriyar yayi alkawarin amincewa da duk takardar yarjeniyar ta Paris kafin wani taron da za a kara yi a Kasar Morocco a karshen shekarar nan. A watan Nuwamban bana dai za a kara gudanar da irin wannan taro na Majalisar dinkin Duniya game da sauyin yanayi a birnin Marrakesh na kasar Morocco.

Shugaba Buhari na Najeriya ya bayyana cewa wannan na daga cikin yunkurin sa na kawo gyara a game da sauyin yanayin a duniya, har ta sa ya jagoranci taron. Kuma, shugaban kasa ya yaba da kokarin Shugaban kasar Faransa watau Francois Hollande wajen ceto tafkin Chadi mai tsotsewa.

Adesina ya bayyana cewa shugaban kasa yace kasar sa za ta dage wajen duba wannan matsalar, yanzu haka an nada kwamiti da za tayi wannan aiki. Yanzu haka ana kokarin share yankin Ogoni da mai ya bata.

The post UN: Shugaba Buhari ya sa hannu a wata yarjejeniya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cQLvPG
via IFTTT


SHARE THIS
Previous Post
Next Post