– Ricikin da ya afku a jam’iyyar APC na jihar Delta ya dada tabarbarewa a ranar Talata
– Mambobin kungiyoyin adawa sun yi arangama a sakatariyar jam’iyyar, sunyi musayar wuta
– Yan sanda sun kama wasu daga cikinsu sun kuma rufe sakatariyar
Hukumar yan sandan jihar Delta sun kama wasu mambobin jam’iyyar All Progressives Congress
Ance magoya bayan kungiyoyin biyu sun samu arangama a sakatariyar jam’iyyar dake Asaba, babban birnin jihar a ranar Talata, 20 ga watan Satumba, jaridar Vanguard ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Manyan kamfanoni zasu zuba hannun jari a Najeriya
Jam’iyyar a jihar ta shiga rikicin shugabanci a tsakanin magoya bayan Olorogun O’Tega Emerhor da magoya bayan dayan kungiyar Spanner Okpozo, wani sanatan jumhuriya ta biyu.
Ance yan baranda dauke da muggan makamai harda bindigogi sun mamaye sakatariyar. Ana zargin sun kai hari ga mambobin kwamitin da’a jihar da suka gana da la’akari da rahoton ayyukan jam’iyyar kan wasu mambobi.
Yan barandan da ake zargin magoya bayan yan kungiyoyin ne sun yi barin wuta.
KU KARANTA KUMA: Direban Shugaba Buhari ya dawo da kudi a Saudiya
Manyan shiryayun jami’an yan sanda sun isa gurin sun kuma kama wasu tare da rufe sakatariyar don guje ma ci gaban arangamar.
Wata majiya da yayi Magana a kan al’amarin yace an kai wadanda aka kama hedkwatan yan sanda don amsa tambaya.
Da yake tabbatar da lamarin, jami’in dake kula da alakar mutane, Celestine Kalu ya bayyana cewa har yanzu ana bincike a kan al’amarin.
The post Yan sanda sun kama mambobin jam’iyyar APC, saboda sun aikata wannan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2dk7lH2
via IFTTT