An bukaci Hadi Sirika yayi bayanin sayar da filayen jiragen sama

– Kungiyar kula da fansho ta hukumar sufurin jiragen sama ta kasa, ta bukaci karamin ministan sufuri, Sanata Hadi Sirika, ya fito fili ya bayyana tsarin da gwamnati ta yi na sayar da manyan tashoshi

– Ko filayen sauka da tashin jiragen kasar nan hudu, wadanda suka hada da Legas, Abuja, Kano da Fatakwal.

Sanarwar da shugaban kungiyar, Kwamred Rasaki Ope, da Sakataren mulki, Emeka Njoku suka sanyawa hannu, ta ce hakan zai taimaka wajen tantance kalubalen tsaro, ganin yadda tashoshin za su kasance karkashin ikon kamfanoni masu zaman kan su.

A wani labari mai kama da wannan kuma a watan da ya shude ne Hukumar yaki da rashawa masu tashe watau hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kai farmakin bincike ofishin ajiye kayayyakin jirgin sama watau National Aviation Handling Company NAHCO da ke babban filin jirgin sama Murtala Muhammed a Jihar Legas.

Game da Jaridar Punch, an gudanar da binciken ne ranan alhamis dinda ya gabata na misalin awa 3, yayinda jami’an Hukumar EFCC ta gudanar da bincike mai zurfi akan na’urar komfutan su da kuma ofishin dubin tasarufi.

Wata majiya a rahoton tace mana daga cikin ma’aikatan da aka bincika sune sakataren kamfanin, shugaban bangaren duban tasarrufin ciki da wasu manyan ma’akatan kamfanin. Ta kara da cewa ana kyautata zaton anyi binciken ne bayan Koran manyan ma’aikatan wurin da akayi a ranar litinin da ya gabata

“Sun binciki sakataren kamfanin, da shugaban ma’akatan akawu da tattalin arziki, da ayyukan amfani,da kayan jirgi kuma basu bar wurin ba har misalign karfe 8 na dare.”

The post An bukaci Hadi Sirika yayi bayanin sayar da filayen jiragen sama appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cr3Voy
via IFTTT


SHARE THIS
Previous Post
Next Post